Ba mu da shirin kara farashin man fetur-IPMAN

Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta musanta labarin da ke cewa tana shirin kara farashin man fetur.

Shugaban kungiyar reshen jihar Enugu Mr Chinedu Anyaso ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai, yana mai cewa akwai bukatar jama’a su yi watsi da wannan labari.

Ya ce basu sami wani umarni ko shawarar kara man fetur daga kamfanin mai na kasa NNPC ba don haka babu wani dalili da zai sanya su kara farashin man fetur din a halin yanzu.

Bayanin nasa na zuwa ne dai-dai lokacin da jama’a suka fara sayen man fetur da yawa don adanawa, saboda tsoron karin farashin man kamar yadda ake yadawa.

 Ya ce a maimakon kara farashin man yana da hasashen cewa za’a sauke farashi ne idan har matatar mai ta dangote ta fara tace man da ya kai ganga dubu 650 kowacce rana.

Yace matatar man ta dangote da gyaran matatar mai ta Fatakwal zasu zamewa ‘yan Najeriya rahama a fannin samun rangwamen tsadar farashin mai.

 

 

 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp