Sarkin Kano na 14 ya caccaki APC kan zaben Kano


Sarkin Kano na 14 , Muhammadu Sanusi II, ya caccaki ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC, a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, kan kin amincewa da kayen da yasha tun da farko.

Ya bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo na karatun da yake gabatar wa a shafukan sada zumunta.

Yace, tafiyar dan adawar kotun koli da ta daukaka kara, inda ya kai ga shan kayi, hakan ya nuna karara bai yadda da kaddara ba.

"Sun so su kwaci abinda mutane suka zaɓa da ƙarfi ta hannun Alkalai."

"Dimokuraɗiyya ake, kuma al'umma su suka zabi abin su, hanasu abinda suka zaɓa zalunci ne." inji tsohon Sarkin.

Post a Comment

Previous Post Next Post