Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da satar janareta da batirin da ke haska futilun masallaci mai amfani da hasken rana a wani masallaci da ke Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Mansir Hassan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Kaduna ranar Asabar.
Mansir ya ce jami’an tsaro sun kama fara kama daya daga cikinsu mai suna Basiru Rabiu da ake zargin a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Hunkuyi.
Sanarwar ta bayyana cewa yadda aka hangi mutumin na labewa tare da yin kwanto a kusa da Masallacin Juma'a suka nuna shakku kuma aka kama shi.
Yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa laifin cewa ya saci janareta da batir mai amfani da hasken rana a masallatan kauyen Hunkuyi da Nahuce.
Inda ya tabbtar da cewa ya sayar da kayan da ya sata ga wani mutum msi suna Mansir Umar wanda shi ma yake a hannun jami’an tsaron.