Abba ya nada Ganduje mukami a Kano


 Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya sanar da nada tsaffin gwamnonin jihar Kano, matsayin mambobin zauren dattawan jihar Kano.



Yayin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Gwamna Yusuf ya ce zauren zai kunshi tsaffin gwamnonin da mataimakansu da tsaffin shugabannin majalisa da mataimakansu da tsaffin alkalan kotun koli da na kotun daukaka kara 'yan jihar Kano da tsaffin sanatoci da malaman addini. 

Labari mai alaka: Martanin Abba Gida-Gida kan hukuncin kotun koli

Gwamnan ya dora wa zauren alhakin bai wa gwamnati shawara ta karshe kan duk wani muhimmin batu da ya taso wa jihar Kano.


Labari mai alaka: Yadda magoya bayan NNPP suka yi murna a Kano

3 Comments

  1. Masha Allah, Alhamdullah, Allah ya hada kawunansu da Al,ummar najeriya bakidaya.

    ReplyDelete
  2. Kai abu yayi kyau wlh allah yasa hakan zama silar hadin kansu baki daya

    ReplyDelete
Previous Post Next Post