Tsadar shinkafa 'yar Hausa ta gigita mutanen Kano

 

dcl hausa

Farashin Naira dubu 47,500 na buhun shinkafar gida ya ɗaga hankalin al'ummar Kano.

Wani bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa buhun shinkafa ta gida a yanzu ana siyar da ita kan N47,500.


Wani dan kasuwan shinkafa mai suna Alhaji Maikano Bello ya ce a zancen nan da ake, ana sayar da ton daya na shinkafa akan naira N450,000 sabanin N320,000 a watan Disamba na shekarar da ta  gabata da aka sayar.


Alhaji Mai-Kano Bello ya yi bayanin cewa yawaitar buqatar shinkafar ce ta jawo tsadar da ake fama da ita a dan lokacin nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post