'Yan ta'adda sun kai hari sansanin sojoji a Katsina

'Yan ta'adda sun kai hari a sansanin sojoji da ke kauyen Nahuta na karamar hukumar Batsari a jihar Katsina

Majiyar DCL Hausa ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 11 na daren Lahadi wayewar Litinin, inda maharan suka shiga cikin gari suka debi dukiyoyin al'umma.

Bayanai sun ce maharan sun yi nasarar kona motocin sojojin guda biyu.

Kazalika, an ga wasu daga cikin mutanen kauyen Nahuta su na barowa a cikin motoci su na dawowa Batsari a wani abu kama da gudun hijra.

Bai dai fi kilomita 7 daga kauyen Nahuta zuwa cikin garin Batsari.

Post a Comment

Previous Post Next Post