Sanata Ali Ndume ya gargadi Tinubu kan mayar da CBN da FAAN zuwa Lagos.

 Sanata Ali Ndume ya gargadi Tinubu kan mayar da Wasu ofisoshin CBN, da Ma'aikatar FAAN zuwa Lagos.  Sanata Ali Ndume, ya gargadi Shugaban Najeriya Bola Tinubu cewa za a samu matsala a siyasance idan har ya dage sai ya koma wasu ma’aikatun Babban Bankin Najeriya (CBN) da hedikwatar Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN). zuwa Legas.


Ndume ya bayyana haka a wata hira da Yayi da manema labarai inda yake bayyana rashin amincewa da wannan mataki na shugaban kasa Tinubu domin wannan ba abune da zai haifarda  da mai ido ba a siyasance. 


Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya ne babban bankin kasa CBN, a wata sanarwa ta cikin gida tace, ta  mayar da wasu ofisoshinta zuwa Legas saboda cunkoson da wasu ma’aikatu ke yi.


Gwamnatin ta sanar da cewa za ta mayar da hedikwatar FAAN domin tabbatar da gudanar da ayyuka na musamman da kuma rage kashe kudade.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post