Gwamna Raɗɗa ya umarci jami'an gwamnatinsa su ayyana kadarorin da suka mallaka


Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya bayar da tabbacin cewa duk masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati a jihar za su bayyana kadarorin su.

Raɗɗa ya bayar da wannan tabbacin ne a jiya Litinin a lokacin da ya karbi baƙuncin shugaban hukumar da’ar ma’aikata, Barista Murtala Aliyu Kankia, a fadar gwamnatin jihar.

A jawabin nasa shugaban hukumar da’ar ma’aikata, Barr. Aliyu Kankia ya bayyana irin rawar da Ofishin sa ke takawa, ba wai kawai sa ido kan bayanan kadarori ba, har ma da tabbatar da bin ka’idojin na da'a ga jami’an gwamnati.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp