Jami'an DSS sun cafke shugaban Miyetti Allah na ƙasa


Jami’an tsaro na farin kaya, sun kama shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo.

Rahotanni sunce kamun nasa ya biyo bayan kirkiro wata ƙungiyar yan sakai da Miyetti Allah ta ƙirƙira jihar Nasarawa.

An cafke Bodejo a yau Talata a babban ofishin Miyetti Allah da ke kusa da Cocin Goshen da misalin karfe 3:40 na yammacin yau Talata.

Post a Comment

Previous Post Next Post