Ana zargin kwamishina da mallakar digiri 'dan Kwatano' Taraba


Ana zargin kwamishinan matasa da ci gaban wasanni na jihar Taraba Joseph Joshua da mallakar digiri na bogi daga wata jami'a a jamhuriyar Benin.

Zargin yana kunshe ne a cikin wata takardar ƙorafi da aka rubuta zuwa ga hukumar tsaro ta farin kaya da rundunar yan sandan jihar.

Wani lauya mai zaman kansa a jihar, Nasiru Muhammad, ne ya rubuta takardar koken a ranar 15 ga watan Janairu a madadin wani mai fafutuka Sulaiman Adamu.

Post a Comment

Previous Post Next Post