Gwamnatin jahar Taraba ta haramta amfani da babura kowane iri a cikin babban birnin jihar daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe.
A sanarwar da ta fito bayan taron kwamitin harkokin tsaro da gwamna Agbu Kefas ya naɗa ta ce an ɗau Matakin ne a kokarin kawar da ayyukan bata gari a fadin jahar baki daya.
A yan makwanni da suka gabata anyi wa wani ma'aikacin gwamnati kisan gilla ta amfani da babur kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito.