Tinubu na son a sulhunta tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Ganduje da Kwankwaso 

Shugaba Tinubu ya fara yunkurin sasanta jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabi'u Kwankwaso da kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje.

A cewar jaridar Daily Trust wasu majiyoyi sun tabbatar mata a jiya Litinin cewa Tinubu ya bayyana aniyarsa ga shugabannin biyu na su sasanta kansu.

Wasu majiyoyi na kusa da Ganduje sun tabbatar da cewa Tinubu ya bukaci shugaban jam’iyyar da ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kano ranar Alhamis mai zuwa, tn are da fara aikin hadin kai a tsakaninsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post