Tinubu yabar Najeriya zuwa Kasar Faransa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yammacin Larabarnan ya bar Abuja zuwa Paris, babban birnin kasar Faransa, don wata ziyarar sirri.
A wata sanarwa da mai bawa shugaban kasar shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce shugaban zai dawo Najeriya a makon farko na watan Fabrairu.
Ajuri Ngelale ya bayyana cewa shugaban Zai yi ziyarar ne zuwa birnin Paris din don wata ziyarar sirri Wanda Ake sa ran zai shafe fiye da mako guda.