Matashi mai shekaru 35 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 55 fyade har ta mutu


Kotun Majistare da ke zamanta a birnin Akure na jihar Ondo ta tsare wani matashi mai shekaru 35 mai suna James Emmanuel bisa zargin yi wa wata tsohuwa mai kimanin shekaru 55 mai suna Deborah Abiodun fyade har ta mutu.

'Yan sanda dai ne suka kama matashin bisa zarginsa da wannan aika-aika ga matar da take abokiyar aikinsa a ranar 17 ga watan Janairun, 2024 a yankin Oke-Edu na jihar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa bayan James ya yi wa matar fyade, tana magashiyyan, ya rotsa mata dutse a kai, ya yasar da gawarta cikin juji.

Kotun dai ta umurci da a cigaba da tsare James a gidan gyaran hali, har sai ranar 27 ga watan Maris, 2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post