Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON)ta sanar cewa hukumomin Saudiyya sun yi ragin kudin aikin Hajjin bana 2024 ga duk masu son sauke farali.
NAHCON ta ce shugabata, Jalal Ahmad Arabi, ne ya mika bukatar a yi ragin inda ya ce ragin ya shafin kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake yi wa alhazai a kasar ta Saudiyya.
Kakakin NACHON, Fatima Sanda Usara ta sanar a ranar Laraba cewa a sakamakon haka, Saudiyya ta rage “Dala 138 daga kudin tikitin jirgin da aka biya Hajjin shekarar 2023, masauki a Madina da aka saba biyan Riyal 2,080 ya koma 1,665, masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.