Dan majalisa a Kano ya dauki nauyin yi wa yara kanana kaciya

Dan majalisar wakilai da daga karamar hukumar Fagge a jihar Kano Mohammed Bello Shehu ya dauki nauyin yi wa yara kanana kaciya a mazabar da yake wakilta.

Wannan yunkuri dai ya sa masu ruwa da tsaki na yankin Fagge da kewaye a jihar ta Kano suka sa kafa suka shure, su na ganin cewa kamar ba wannan al'umma ke bukata ba.

A al'adance dai, al'ummar Hausawa na yi wa 'ya'yansu kaciya a zamanin sanyi.

Dan majalisar da yake a jam'iyyar NNPP ya bugi kirjin daukar nauyin yara sama da 1,000 da za a yi musu kaciya a mazabu 11 da yake wakilta.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa har ma an kaddamar da wannan aiki a ranar Asabar a cibiyar kiwon lafiya ta Ofishin Galadima da ke mazabar Fagge B.

Wannan lamari dai ya sa ana ta ce-ce-kuce har wasu na ganin kamar dan majalisar ba zai iya cika alkawarin da ya dauka ba a zamanin yakin neman zabe.

Post a Comment

Previous Post Next Post