Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU ta ce har yanzu ba a
fara sakin Albashin watanni 4 da shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci a biya su.
Kimanin watanni biyu cif-cif tun bayan da
shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da a saki albashin watanni
hudu da aka hana malaman jami'o'in Nijeriya sakamaon yajin aikin da suka
tsunduma, kungiyar malaman jami'o'i ta (ASUU) ta ce har yanzu mambobinta ba su
karbi albashin ba.
Shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce har
yanzu gwamnati ba ta aiwatar da mafi
yawan bukatun da suka yi jarjejeniyar za a biya wa ya'yanta.
Wannan na zuwa ne bayan da yan kungiyar ta ASUU suka rika
korafi kan yadda kudaden tafiyar da majalisun dokokin kasar biyu ya zarta wanda
aka ware musu cikin kasafin kudin bana.