Da dumi-dumi: Betta Edu ta isa ofishin EFCC

 


Dakatattar ministar jin kai da yaki da fatara, Dr Betta Edu, ta isa hedikwatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), bisa zarginta da hannu a badakalar naira miliyan 585.

Idan dai za’a iya tunawa, shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Dr Betta Edu akan mukaminta bisa wata badakalar kudin da suka kai Naira milyan 585.

An dai zargi ministan da tura wasu kudade a wani asusun banki na wani mutum, wanda hakan ya saba dokar kasa.

Dr Betta Edu, ta zama minista ta farko da aka dakatar daga aiki tun bayan rantsar da mambobin majalisar zartarwar ta tarayya a watan Agustan shekarar da ta gabata.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp