Jami'ar BUK da ke Kano ta musanta batun nan da ke cewa tana da furofesoshi na bogi har kusan 20.
Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Sagir Abbas ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba ma manema labarai a Kano.
“Mun ga wasu labarai da ke yawo a kafafen sada zumunta wai akwai wasu farfesoshi na bogi har guda 20 da ke aiki a jami’ar.
Abbas ya yi kira ga mutane da su yi watsi da wannan labarin.
Sanarwar ta ƙara da cewa kwanan nan jami'ar ta kasance a matsayi ta 5 mafi inganci a Nijeriya.
Category
Labarai