Murna bayan da Abba ya kayar da Gawuna a kotun koli

 


a tabbata Abba Zama Daram! Alkalan kotun kolin Najeriya sun bai wa duniya mamaki bayan da suka sanya kafa suka yi fatali da hukunce-hukuncen da kotun sauraren kararrakin zabe da ta daukaka kara suka yi, wanda ya kwacewa Abba Nasarar da tun farko hukumar zabe ta bashi.

Alkalan  kotun koli sun ce akwai lam’a cikin hukunce-hukuncen da kotunan suka yanke da farko, kuma babu yadda za’a yi su zuba idanu suna kallon wannan gagarumin kuskure ya wuce tun da dai ai su ba makafi bane, a don haka sun dawo wa da Engr. Abba Kabir Yusuf kuri’unsa  dubu 165 da kotun sauraren kararrakin zabe ta debe wa Abba tun da farko.

Alkalan sun ce sun jinge nasarar da kotunan da suka gabata suka bai wa jam’iyyar APC ta Dr. Nasiru Gawuna, kuma ma kada su sake jin an tayar da wannan magana ko da teburin mai shayi ne saboda kuskuren da kotunan biyu da suka gabata suka yi. 

Da ma dai Engr. Abba Kabir Yusuf shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar da kuri’u sama da miliyan daya, kuri’un da ake ganin kakaf Najeriya babu wani gwamna da ya taba samun makamantan su a tarihi. To amma duk da wannan hukunci, magoya bayan Dr. Gawuna wadanda a watannin da suka gabata suka yi ta mafarkin ganin gwanin na su a gidan Gilas, sun bayyana wa DCL Hausa martaninsu.

Da wannan hukuncin dai siyasar Kwankwasiyya ta kara samun karfi a jihar Kano kuma tuni magoya bayan jam’iyyar suka fara murna tare da yi wa juna farin cikin tsallake siradin da ya so ya yi awon gaba da nasarar da INEC ta ayyana musu tun da farko. Jami’in yada labarai na jam’iyyar NNPP Nuhu Yankaba shi ne ya fara bayyana wa DCL Hausa murnarsa.

To yanzu ko’ina makomar Dr. Nasiru Yuzusf Gawuna da jam’iyyarsa ta APC ke nan? Ga babban lauyan Najeriya Professor Lawan Yusufari.

A yanzu dai za a zura ido don ganin irin salon da siyasar jihar Kano za ta dauka bayan wannan hukunci da aka kwashe wata da watanni ana jiran zuwan sa zuwansa.  


A tarihin gwamnonin da suka Mulki jihar Kano ta hanyar siyasa Engr. Abba Kabir Yusuf shi ne na. Kafin wannan nasar da kotun koli ta tabbatar masa, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ne aka fara zaba a shekarar 1979 a jam'iyyar PRP, sai Alhaji Abdu Dawakin Tofa sai kuma Alhaji Sabo Bakin Zuwo, dukkaninsu 'yan jam'iyyar PRP. Sanata  Kabiru Ibrahim Gaya ya take musu baya a jam'iyyar  NRC. Daga nan sai Rabi'u Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da kuma Abdullahi Umar Ganduje

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp