A yau Gawuna da Abba Gida-Gida za su san makomarsu a mulkin Kano

 


Rana ba ta karya, a yau ne kotun kolin Nijeriya za ta kawo karshen turka-turka da nuna wa juna yatsa da jam’iyyar APC da NNPP suka dade suna yi kan sahihancin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a watan Maris na shekarar da ta gabata.

Engr. Abba Kabir Yusuf, shi ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’a sama da miliyan 1 yayin da babban abokin takararsa na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya samu kuri’u kimanin 890,000.

To sai dai kuma yayin da Abba da magoya bayansa ke tsaka da murnar samun wannan nasara, kwatsam sai kotun sauraren kararrakin zabe ta ce ba shi ne ya sami nasara ba saboda ta gano kuri’a sama a dubu 160 da aka ce ba su da shaidar tambarin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, don haka na sata ne.

Wannan dai a ganin wasu na zama tamkar wani sabon abu, la’akari da yadda sad‘arar kundin dokar zabe ta 2022 ta ce ko da babu tambarin hukumar INEC a jikin takardar zabe matukar baturen zabe ya kirga ta to tana a matsayin halastacciyar kuri’a.

Jam’iyyar NNPP ba ta amince da wannan bayani na kotu ba don haka ta garzaya zuwa kotun daukaka kara, amma kuma can din ma da alama ba ta sauya zani ba, kasancewar alkalan kotun sun tabbatar da hukuncin Tribunal inda anan ma suka kara da cin tarar Abba Kabir Yusuf kudi har naira miliyan guda ladan bata wa Nasiru Yusuf Gawuna lokaci.


Kotun ta kuma kara fayyace manyan dalilan da suka yi wanchakali da nasarar Abba ciki kuwa har da rashin mallakar katin zama dan jam’iyyar NNPP kafin tsayawa takara, abin da ke nufin kai tsaye ma jam’iyyar ba ta da dan takara.

To amma abin da ya daure wa ‘yan jam’iyyar NNPP da dama kai shi ne yadda kotun ta iya bayyana wannan a matsayin hujjar kwace nasarar, kasancewar ta sha yanke hukunce-hukunce da ke cewa batun zama dan jam’iyya ko akasin haka kafin tsayawa takara ba hurumin kotu ba ne hurumin ‘ya’yan jam’iyya ne.

Wani babban da ya janyo cece-kuce shi ne yadda takardar hukunci ta nuna cewa Abba Kabir Yusuf ne ya yi nasara a kotun ba Gawuna ba, abin da wasu suka ce kalaman alkalan ya sha bambam da rubutunsu, lamarin da ya kara haifar da rudani tsakanin siyasar jihar Kano mai matukar muhimmanci a arewacin Nijeriya.

Maganin ka da ayi kar a fara! Watakila tun a wannan karin magana ya sa NNPP ta yi gaggawar kai kokenta gaban kotun koli don ta fayyace me wannan shubuha ke nufi da kuma ba ta karin hujjoji na ganin darikar siyasar Kwankwasiyya ta ci gaba da mulkin jihar Kano.

Shin mene ne manyan korafe-korafen jam’iyyar APC mai kara?

APC na zargin jam’iyyar NNPP da aringizon kuri’a da kuma amfani da kuri’un da ba su da inganci wajen kara yawan kuri’un da Abba Kabiru Yusuf ya samu.

Tana kuma zargin NNPP da hada kai da matasa wajen tayar da tarzoma a runfunan zaben da APC din ke da rinjayen magoya baya, a yayin da take ganin ya dace hukumar zabe ta ayyana zaben gwamna a matsayin wanda bai kammala ba, la’akari da cewa an ayyana na ‘yan majalisu da dama a matsayin wanda bai kammala ba, kuma a tare a ka yi su.

Korafi na uku shi ne yadda NNPP din ta gaza mika sunan Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takara kafin cikar wa’adin da hukumar INEC ta kayyade.

Akwai kuma yadda shi gwamnan na Kano ya mallaki katin shaidar zama dan jam’iyyar NNPP bayan ya zama gwamna, abin da suka ce ya zama gwamna karkashin inuwar jam’iyyar ta NNPP amma lokacin kuma yana PDP.

Tawagar lauyoyin jam’iyyar ta APC sun biyo bayan wadannan hujjoji da suka bayyana wa kotu da bukatar ta kwace nasarar da Abba ya samu kuma ta mika ta ga Nasiru Gawuna ba tare da ba ta lokaci ba.

NNPP ta musanta

Da alama wadannan maganganu ba su zauna dai-dai a kunnuwan lauyoyin jam’iyyar NNPP musamman Bashir Tudun Wuzurci ba, kasancewar ya soke su ta hanyar fayyace wa kotu cewa babu wata ingantacciyar magana a ciki, kuma ma yana bukatar kotun ta yi watsi da su.

Da farko dai Barrista Bashir Tudunwuzurci ya ce ba gaskiya ba ne cewa NNPP din ta yi amfani da kuri’un bogi, a cewarsa ba ya cikin hakkin jam’iyya duba takardar kuri’ar da ke dauke da tambari ko akasin haka don haka idan akwai mai laifi bai wuce hukumar ta INEC ba, kuma bai kamata a hukunta jama’ar Kano da laifin da hukumar INEC din ta aikata ba.

Kan batun rashin katin zama dan jam’iyya kafin zabe kuwa, lauyan ya dage kan cewa Abba Kabir Yusuf yana da katin zama dan jam’iyya kafin ma ya tsaya takara don haka wannan farfaganda ce kawai ta abokan hamayya.

Yayin da yake zuba ingilishi a gaban alkalai, lauyan na NNPP ya ce jam’iyyar ta mika sunan Abba cikin lokaci kamar yadda doka ta tanada, don haka babu wani dalili da APC ta dogara da shi kan wannan zargi.



NNPP na ganin cewa karar da APC ta shigar bata lokaci ne da kuma yunkurin jefa kanawa sama da miliyan 1 da suka zabi Abba cikin fargaba don haka akwai bukatar kotu ta yi watsi da wannan kara.

Bahaushe yace ranar wanka ba’a boyen cibi, yau ne dai kowanne daga cikin mutanen da ke hammaya da juna zai san makomarsa kuma kowanne bangare na nuna kwarin gwiwar cewa kotun koli za ta biya masa bukata.

Yayin tattaunawarsa da DCL Hausa, lauyan masu kara wato APC Barista Abdul Fagge ya ce suna da yakinin a yau din ma sune da nasara kamar yadda suka samu a baya saboda hujjoji masu karfi da suka rika.

To amma da yake mayar da martani , a lokacin da wannan kafar yada labarai ta tuntube shi lauyan jam’iyyar NNPP ta Abba Gida-Gida Barista Bashir Tudunwuzurci ya ce yana da yakinin cewa Kotun Koli za ta yi watsi da wannan kara, la’akari da hukunce-hukunce makamantan wannan da ta yanke a baya.


Ga wasu abubuwa 6 masu muhimmanci kan wannan shari’a 

1-Wannan ba shi ne karon farko da kotun koli ke yanke hukunce-hukunce da ke da alaka da zaben gwamna ba.

2-Kotun kolin ta sha yin watsi da kararrakin da suka shafi rashin katin zama dan jam’iyya ga dan takara, wanda tace wannan abu ne na cikin gida, ma’ana dai ba ta da hurumi.

3-To sai dai wannan kuma ba zai zame wa jam’iyyar NNPP sandar duka ba, ganin cewa kotun daukaka kara ma ta sha yanke irin wannan hukunci amma a kan tasu karar ta sauya matsaya.

4-Hukumar INEC tana cikin wadanda suka daukaka kara, amma daga baya ta janye, shin me hakan ke nufi ga makomar NNPP a kotu? Kotun Koli za ta bayar da wannan amsa. 

5- Kotun Koli ta sha sauke wasu gwamnoni masu ci a baya. Amma babu tabbas a wannan karan ko Engr. Abba Kabir Yusuf zai iya tsallake wannan siradin.

6-Dan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ba ya cikin wadanda suka shigar da kara, amma kuma yana cikin masu murnar jiran karbar shugabanci.

Sa’o’i kalilan suka rage kotun koli ta rufe babin ja-in-jar da jam’iyyun biyu ke yi, yayin da jama’ar Kano ke cike da zullumin me zai je ya dawo game da hukuncin mai cike da sarkakiya.

Shari’a dai mace ce da ciki, ba a san me za ta haifa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp