Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da a fitar da kudi Naira milyan 173 don aikin samar da lantarki ta hasken rana a babban asibitin da ke Dutse, babban birnin jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar Sagir Musa ya sanar da hakan ga manema labarai, inda ya ce majalisar zartarwar jihar ce ta amince da hakan bayan taron da ta gudanar a ranar Alhamis.
Kwamishinan ya ce wannan matakin ya biyo bayan kudirin Gwamnan jihar Umaru Namadi na kyautata babban asibitin jihar don samar da kiwon lafiya mai inganci ga al'ummar jihar.