Sarkin Katsina ya sanar da korar shirin AGILE bisa saba ka’idojin Musulunci

 

Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya sanar da korar shirin inganta ilmin 'ya'ya mata na AGILE daga jihar Katsina.

Mai Martaba Sarkin ya ayyana korar ne ga manema labarai a fadarsa, a lokacin da ya ke wasu nade-naden sarautu a karshen mako.

Jaridar yanar gizo ta Mobile Media Crew ta rawaito Sarkin na cewa, korar shirin ya biyo bayan keta wasu ka’idoji addinin Musulunci da shirin ke kokarin yi a jihar da kuma zargin kokarin bata tarbiyar 'ya'ya mata da ke karatu a makarantu

Ya ci gaba da cewa shirin na kokarin wuce gona da iri wanda a matsayinsu na iyayen kasa, ba za su lamuncewa hakan a cikin kasa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post