Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya karbi wani rahoto da ake zargin wani malamin makarantar sakandare mai suna Lawal Ibrahim, da yunkurin keta haddin wata dalibar makarantar da yake koyarwa.
Malamin wanda a da shi ne shugaba, wato 'Principal' na makarantar sakandaren garin Dantankari dake karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina, ma'aikaci ne da Ma'iakatar Ilimi ta jihar Katsina.
Gwamnan Dikko Radda ya umurci kwamishinar ma'aikatar ilmin firamare da na sakandare ta jihar da ta gaggauta dakatar da wannan malami mai suna Lawal Ibrahim sannan a kaddamar da bincike a kan lamarin, ta kuma mika rahoton binciken ga gwamnan.
Haka kuma Gwamnan ya umurci kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina da ya binciki lamarin, tare da bincikar Baturen 'yan sandan(DPO) na karamar hukumar Dandume wanda ake zargi da karbar rashawa da kuma kokarin yin balulluba kan batun.
Gwamnan ya bukaci shi ma Kwamishinan ya gabatar masa da sakamakon binciken.
Wannan Matakin yayi dai dai
ReplyDelete