Da N800 muke ciyar da duk kare daya da muke aiki da shi, yayin da muke ciyar da fursuna da N750 a kowace rana - Gwamnatin Nijerya

Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta kasa Halliru Nababa ya ce hukumar na kashe kudi masu yawa don ciyar da karnukan da ake aiki da su, fiye da yadda ake kashe wa mutanen da ke tsare a gidan yari.

Halliru Nababa ya sanar da hakan ne a gaban kwamitin majalisar dokokin Nijeriya da ke kula da harkokin cikin gida son kare kasafin kudin shekarar badi, 2024.

Ya ce hukumar ta rubuta wa ministan harkokin cikin gida, inda take neman da a kara yawan kudin da ake ciyar da 'yan gidan yari daga Naira 750 zuwa 3,000 a rana.

Shugaban hukumar ya ce har yanzu su na jiran amincewar ma'aikatar harkokin cikin gida kan wannan bukata ta su, inda ya bukaci majalisa ta sa baki don a amince musu su yi wannan karin.

Halliru Nababa ya ce a shekarar 2023, Nijeriya na da mutane 81,354 da ake tsare da su a gidajen ysrin kasar.

Hukumar ta sanar cewa tana ciyar da duk kare daya da ake aiki da shi a hukumar kan kudi Naira 800 duk rana.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp