Kotu ta yi hukunci ga mutumin da ya kashe abokinsa saboda Naira 100 a Zamfara

Babbar kotun jihar Zamfara ta yanke hukuncin kisa ga wani mutum mai suna Anas Dahiru bisa samunsa da laifin kashe abokinsa saboda takaddamar kudi N100.

A shekarar 2017 ne dai aka gabatar da Anas a gaban kotun, inda ake zarginsa da kisan abokinsa Shamu Ibrahim kan Naira 100, inda ya daba masa wuka.

Da ya ke karanta hukuncin, Alkalin kotun Mai Shari'a Mukhtar Yusha'u, ya ce wanda ake zargin Anas Dahiru da ke a unguwar Dallatu da ke cikin birnin Gusau ya caka wa abokinsa Shamu wuka a lokacin da suke takaddamar kudi Naira 100.


Post a Comment

Previous Post Next Post