Jaridar Daily Trust ta gano cewa a cikin daftarin kasafin kudin shekarar badi, 2024 d shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa, babu kason aikin samar da lantarki a Mambila da ke Gembu jihar Taraba.
Sai dai an ware wa ma'aikatar makamashi da ke kula da sha'anin lantarki kudi Naira milyan 400 don shirya taruka a cikin shekarar ta 2024.
Aikin samar da lantarki na Mambila dai ya haddasa ce-ce-kuce a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, da ake kyautata zaton idan an yi shi zai samar da megawatts 3,050 ga Nijeriya.
A shekarar 2017, majalisar zartarwar Nijeriya ta amince da fitar da kudi Dalar Amurka 5.729 kwatankwacin Naira Tiriliyan 1.140 don gudanar da aikin.