An gano inda ake hada-hadar cinikin kodar bil'adama a Abuja


Wani zurfaffen bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya gano inda ake sayar da kodar bil'adama a babban birnin tarayya Abuja.

Binciken ya gano cewa a kasuwar ta bayan fage, ana sayar da duk koda daya kan kudi Naira milyan daya.

Kazalika, an gano yadda ake yaudarar mutane musamman masu karamin karfi ta yadda za a ja ra'ayinsu, su sayar da kodar su.

An dai gano cewa wannan sana'a ta jima ana gudanar da ita, musamman a yankin Mararaba da ke kusa da birnin tarayya, amma garin ya ke a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post