Yunkurin ofishin Mai Ba Shugaban kasa Shawara kan harkokin tsaro ne ya sa aka sako daliban jami'ar FUDMA - VC


An sako dalibai mata na Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma kwanaki 74 bayan sace su da 'yan bindiga suka yi.

An dai sace daliban su biyar ne a ranar 03 ga watan Oktoba, 2023. Sai dai daya daga cikinsu ta kubuta kwanaki kadan bayan sace su.

Shugaban jami'ar Prof Armaya'u Hamisu Bichi ya ce tabbatar ko an biya kudin fansa ko a'a, kawai dai ya ce yunkuri da kokarin Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro NSA Malam Nuhu Ribadu ne ya sa aka sako daliban.

Post a Comment

Previous Post Next Post