Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo ya kori daraktoci 33 da ke aiki a karkashin ma’aikatar da yake jagoranta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito karkashin ma’aikatar sufurin jiragen sama mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Odutayo Oluseyi da ya fita a ranar Alhamis.
Korar na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da shugaban kasa, Bola Tinubu ya kori Manajan Daraktan FAAN, Kabir Mohammed; NAMA, Toyib Odunowo; Babban Daraktan NiMet, Farfesa Mansur Matazu; Babban Daraktan Hukumar NSIB, Engr. Akin Olateru da kuma dakatar da babban darakta na NCAA, Kyaftin Musa Nuhu.
Sanarwar ta kara da cewa an yi korar ne domin a kara inganta ma’aikatar ta yadda za a rika gudanar da aiki a cikin tsari mai tsafta.