APC na zawarcin Wike

Jam'iyyar APC ta ce tana nan tana zawarcin tsohon Gwamnan Rivers kuma ministan Abuja a halin yanzu Mr Nyesom Wike zuwa jam'iyyar.

Jam'iyyar ta ce muddin ya karbi tayinta na komawa, zai zama shi ne babban jigo kuma jagoranta a jihar Rivers.

Jaridar Daily Trust ta ba da labarin cewa Wike na yawan nanata cewa shi dan jam'iyyar PDP ne duk kuwa tarnaki da ciwon kan da ake ganin ya ba PDP bayan ya fadi zaben fitar da gwani a zaben shekarar 2023 da Atiku Abubakar ya kayar da shi.

A baya-bayan nan, baraka ta kunno kai tsakanin Wike da yaronsa a siyasa Gwamnan Rivers na yanzu Sim Fubara da hakan ya jaza tsagewar majalisar dokokin jihar gida biyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post