Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC na neman tsohon ministan lantarkin Nijeriya Mr Olu Ogunloye ruwa jallo.
Hukumar na neman tsohon ministan da ya fito daga jihar Ondo ne bisa tuhumar cin hanci da zamba.
A watan Satumbar da ya gabata, EFCC ta tsare Mr Olu kan badakalar Dala bilyan 6.
EFCC ta bayyana hakan a ranar Laraba a shafinta na yanar gizo.
Mr Olu Ogunloye dai ne ministan lantarkin Nijeriya daga 1999-2003 a zamanin wa'adin farko na mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.