Mutanen kauyen Tudun Biri sun maka FG kotu, su na neman diyyar N33bn

Mutanen kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna sun maka gwamnatin tarayya kotu tare da neman diyyar kudi Naira bilyan 33.

Matakin mutanen ya biyo bayan kashe mutane sama da 100 da jirgin sojan Nijeriya ya yi a makon jiya. Sai dai sojojin sun amsa laifin su, sun kuma ce hakan ta faru ne bisa kuskure.

Ibtila'in ya fada wa al'ummar yankin a lokacin da suke bikin Mauludi.

Tuni dai shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umurci da a gudanar da bincike mai zurfi don gano hakikanin abin da ya faru. Sannan ya ma ja kunnen sojojin da sauran jami'an tsaro da kada su kuskura hakan ta sake faruwa a sassan kasar.

Alhaji Dalhatu Salihu ne ya shigar da karar a babbar kotun jihar Kaduna a madadin al'ummar kauyen Tudun Biri ta hannun lauyansu Mukhtar Usman.

Mutanen kauyen na kuma bukatar a ba su hakuri a rubuce a kuma buga a manyan jaridu uku na Nijeriya.

Har yanzu dai ba a kai ga saka ranar da za a fara sauraron karar ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post