Rikicin siyasa ya sa yanzu haka an rusa ginin majalisar dokokin jihar Rivers.
Da sanyin safiyar Larabar nan dai, jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an ga motoci samfurin bulldozer da ke rusa gini a bakin harabar majalisar.
A ranar Litinin din makon nan dai 'yan majalisar 27 cikin 32 suka bar jam'iyyar PDP inda Gwamnan ya ke suka koma APC ta shugaba Tinubu.