Kwastam sun fara binciken jami'ar su da ake zargi da karbar na-goro a filin jirgin Lagos


Wani faifan bidiyo ya bayyana yadda wata jami'ar hukumar kwastam a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos, tana so ala-tilas sai an ba ta na-goro Naira 5,000.

Wani fasinja dai ne, aka gano bidiyon matar da ke sanye da uniform da mukamin anini daya take umurtarsa dole sai ya ba ta kudi kafin ya wuce da kayansa.


Sai dai mutumin ya hakikance cewa ba zai biya N5,000 ba, shi N1,000 zai biya.

Mai magana da yawun hukumar Abubakar Maiwada a cikin wata sanarwa, ya ce ana nan an kaddamar da bincike kan lamarin.

Maiwada ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa wanda aka nema ya ba da cin hancin ne ya nadi bidiyon.

Post a Comment

Previous Post Next Post