Jaridar Daily Trust ta gano cewa yawan amfani da ake da albasar da karancin da ta yi a kasuwanni ne ya sa albasar ta yi tsada.
Binciken ya gano cewa ana sayar da buhun albasar kan kudi Naira dubu 120,000. Sai dai bincike ya gano cewa farashin ya fara sauka bayan da aka fara shigo da 'yar waje daga Gada ta Jamhuriyar Nijar.