JAMB ta kara farashin kudin rajista

Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta Nijeriya JAMB ta sanar da kara kudin rajistar jarabawar da za a zauna a shekarar 2024.

A cikin wata sanarwa daga hukumar, ta ce yanzu za a rika biyan kudin rajistar Naira dubu 7,700 da kuma Naira 6,200 kudin neman share fagen zauna jarabawar ta Mock.

Kafin wannan karin dai, ana sayar da fom din JAMB kan kudi Naira5,700, sai take kamawa 6,700 hada jarabawar Mock.

Hukumar ta ce daliban kasashen ketare da ke da aniyar zuwa Nijeriya su zauna jarabawar za su sayi fom din Dala 30.

Post a Comment

Previous Post Next Post