Hukumar zaben kasar Masar ta sanar cewa shugaba Abdel-fatah Al-sisi ya sake yin nasara karo na uku bayan zaben da aka gudanar makon jiya.
Al-sisi ya zamo shugaban kasar Masar a shekarar 2014, aka sake zabensa a shekarar 2018, sai yanzu da zai ci gaba da jagorantar kasar har zuwa 2029 da kundin mulkin kasar ya ce nan ne magaryar tukewa.
Hukumar zaben dai ta ce Abdel-fatah Al-sisi ya lashe zaben ne da kaso 90% na yawan kuri'un da aka kada.