An damfari 'yan Nijeriya sama da 1,000 da sunan za a ba su aiki a Ingila - IOM

Hukumar da ke kula da masu gudun hijira ta majalisar dinkin duniya IOM ta ce akwai 'yan Nijeriya sama da dubu daya da aka damfara da sunan za a samar musu aiki a kasar Ingila.

Babban jami'in hukumar a Nijeriya Laurent De Boeck ya sanar da hakan a Abuja a lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Mr Boeck ya ce kusan kowanensu ya yi asarar kudin da suka kai darajar Dala dubu 10,000 ta dalilin neman aikin, amma ba a yi kwado da yaro ba kuma ba a bashi gayansa ba.

Mr Laurent ya ce idan suka je ma'aikatun suka gabatar da takardun kama aikin da aka damfare su aka ba su, sai ma'aikatun su ce wannan takarda ba daga gare su take ba.

Ya ce da yawansu suna can sun yi tsuru-tsuru a Ingila ba su da kudin komowa Nijeriya, a yayin da wasu kuma ke kunyar dawowa su tunkari iyalansu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp