Katsina da Yobe ne jihohin da ba su iya rayuwa idan babu kudin FAAC na FG - RahotoRahoton shekara-shekara na karfin hanyoyin samar da kudaden shiga na jihohi a Nijeriya ya nuna cewa akwai jihohin da idan babu daunin gwamnatin tarayya, ba za su iya tsayawa da kafafunsu ba.

Jihohin kamar yadda rahoton ya ce su ne Katsina, Kebbi, Bayelsa, Akwa Ibom, Taraba da Yobe.

Rahoton da aka fitar a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ya nuna cewa jihohin 6 sun gaza samar da kaso 10% na kudaden shiga daga cikin gida IGR a shekarar 2022.

Kudaden shigar jihohi 36 na Nijeriya a shekarar 2022 sun kai Naira Tiriliyan 1.8, inda suka zarta na shekarar 2021 da aka samu Naira Tiriliyan 1.7.

Jihar Lagos dau ce kan gaba wajen tattara kudaden shiga a cikin gida da Naira bilyan 651 sai jihar Ogun ta biyu sai jihar Rivers ta uku.

Post a Comment

Previous Post Next Post