Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta dakatar da tsohuwar ministar harkokin mata a gwamnatin Buhari, Ms Pauline Tallen da karbar duk wani mukamin da ya danganci gwamnati.
A cikin hukuncin da ta yanke a ranar Litinin, kotun ta nuna rashin jin dadinta kan kalaman Pauline Tallen bayan da aka yanke hukuncin da ya danganci jihar Adamawa a shekarar bara.
A baran dai ne kotun ta yanke hukuncin cewa Aisha Binani ta APC ba ta cancanci tsayawa takarar Gwamna ba.
Daga cikin kalaman Pauline Tallen a wancan lokacin, ta ce wannan hukuncin kotu ya yi kama da hukuncin kama-karya.
Shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa Yakubu MaiKyau a lokacin ya nemi Pauline Tallen da ta nemi afuwar ta kuma janye kalamanta, idan ba haka ba, zai maka ta kotu, amma ta kiya, dalilin da ya sa hakan ya kai su kotu.