'Yan majalisa sun kori kwamishinan kasafin kudin daga zauren majalisar dokokin jihar Zamfara



'Yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun bukaci da kwamishinan kudi na jihar Abdulmalik Gajam da ya fita daga zauren majalisar a lokacin da Gwamna Dauda ya gabatar musu da daftarin kasafin kudin 2024.

'Yan majalisar dai sun ce sun dauki wannan matakin ne biyo bayan kin mutunta gayyatar majalisar da suka ce kwamishinan ya yi, na ya je gabansu don kare kasafin kudin shekarar 2024.

Bayan tattaunawa, majalisar ta amince cewa takardar tabbatarwar da ta ba kwamishinan tun da farko, ta janye.

Kamar yadda suka ce, sun gayyaci kwamishinan sau uku don ya je majalisar ya kare kasafin kudin shekarar 2024 na ma'aikatarsa, amma ya ki zuwa, kuma bai bayar da wata hujja mai kwari ba.

Bayan kammala bayyana wadannan dalilai na su, 'yan majalisar sun bukaci kwamishinan da ya fita daga zauren majalisar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp