Ba Faransa ce ke ingiza ECOWAS daukar matakai kan Nijar ba - Ministan Tinubu

Ministan harkokin kasashen waje na Nijeriya Amb Yusuf Tuggar ya sanar cewa babu kanshin gaskiya a zargin da wasu ke yi cewa kasar Faransa ce ke ingiza kungiyar ECOWAS ta dauki matakan kakaba takunkumai ga kasar Nijar tun bayan juyin mulkin soji.

Kungiyar ECOWAS sai ta sanya wasu takunkumai ga kasar Nijar tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohammed a farko-farkon wannan shekara.

Daga cikin takunkuman akwai na rufe kan iyakar Nijeriya da Nijar da yanke wutar lantarki da katse huldar jakadanci da sauransu.

Ministan ya yi wannan furucin ne a wata zantawa da gidan talabijin na Trust Tv.

Post a Comment

Previous Post Next Post