Babban bankin Nijeriya CBN ya yi bitar matsayarsa game da hada-hadar Crypto a kasar.
Babban bankin a ranar Juma'a ya ce ya sauya matsayarsa game da batun Crypto din, ya umurci bankuna da su yi watsi da matakin farko na haramta cinikin crypto, yanzu su ci gaba da yi.
A cikin sanarwar da babban bankin ya aike wa bankuna a fadin Nijeriya ya ce bayan binciken da ya gudanar, ya gano cewa ana bukatar crypto a hada-hadar cinikayya a duniya bakidaya.
A watan Fabrairun 2021 ne dai bankin na CBN ya umurci bankuna a Nijeriya da su kaurace wa duk wata alaka da crypto.