'Yan sanda ba za su fita daga tsarin fansho na 'Contributory Pension Scheme' ba - IGP


Babban sufeton 'yan sandan Nijeriya IGP Kayode Egbetokun ya sa kafa ya shure rokon da 'yan sandan kasar ke yi na a cire daga tsarin fansho na aikin dan sanda.

Babban sufeton 'yan sandan ya ce ana yin wannan tsarin fansho ne da nufin kyautatawa da dadawa 'yan sandan Nijeriya ba wai don a musguna musu ba.

Hakan na zuwa ne duk da kiraye-kiraye da tsoffin 'yan sanda da wadanda ke aiki a halin yanzu ke yi na a cire su daga tsarin fansho na aikin dan sanda.

Majalisar dokokin Nijeriya da ta gabata dai ta zartar da kudirin dokar da ke neman a cire 'yan sanda daga cikin wannan  tsari.

Da ya ke jawabi a hedikwatar 'yan sandan jihar Kwara, Kayode Egbetokun ya ja kunnen 'yan sanda cewa babu alheri a cire su daga wannan tsari.

Ya ce a lokacin da ya kama aiki a matsayin babban sufeton 'yan sandan Nijeriya, ya kafa kwamitin da zai yi bincike mai zurfi game da batun, sai ya gano cewa idan suka fita daga tsarin fanshon 'yan sanda, to za su koma hannun 'yan siyasa ne su yi ta yin yadda suka ga dama da su.

IGP Kayode ya ce idan kuma aka yi haka, tsarin fanshon 'yan sanda zai ta'allaka ne kan yadda kasafin kudin kasa ya kasance, ma'ana, idan gwamnati na da kudi, za ta biya fansho, idan ba ta kudi kuwa, ba za a biya ba.

Babban sufeton 'yan sandan ya ce da zarar an cire 'yan sanda daga wannan tsarin, to za su koma bin bashin fansho na tsawon watanni da gwamnatin za ta gaza biya.

IGP Kayode Egbetokun ya ce yana nan yana tattaunawa da shugaban kasa, na yadda za a kara yawan kudin fansho din. Ya kara da cewa akwai tsarin da ake fatar za a bullo dashi na yadda dan sanda zai yi rika samun fanshonsa mai yawan albashin da ya yi ritaya a kai.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp