Bam ya tashi da masu Mauludi a Kaduna

Rahotannin da jaridar Daily Trust ta samu sun nuna cewa ana kyautata zaton mutane da yawa sun mutu bayan da ake zargin cewa wani jirgin sojin saman Nijeriya ya jefa bam ga wasu mutane da ke bikin Mauludi a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Duk da dai babu cikakken bayanin yadda lamarin ya faru, amma dai wasu rahotanni sun ce mutane kusan 30 sun mutu bayan jefa bam din da misalin karfe 9 na dare.

Mazauna kauyen sun sanar cewa jirgin ya yi ruwan bama-baman ne a lokacin da mutanen kauyen suka tattaru domin su gudanar da bikin murnar haihuwar fiyayyen halitta, manzon tsira 'SAW'.

Ana dai fargabar ban gaba yawan wadanda suka rasu su ya karu.

Ta bangaren gwamnati, Samuel Aruwan da ke kula da ma'aikatar tsaron cikin gida ta jihar Kaduna, ya ce za su yi taron manema labarai nan gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post