Sojin saman Nijeriya sun musanta sakin bam ga masu Mauludi a Kaduna

A cikin wata sanarwa da safiyar Litinin, sojojin sun ce sa'o'i 24 da suka gabata, ba su kai wani samame ta sama a shacin jihar Kaduna ba.

Sojojin a sanarwar da Daraktan yada labarai Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, ta ce ya kamata mutane su san cewa ba sojojin sama kadai ke samame a jirage ba a arewacin Nijeriya.

Sanarwar ta kara jan hankalin 'yan jarida da su rika tabbatar da sahihancin labari kafin su buga.

Jaridar Daily Trust dai ta wallafa cewa ana zargin jirgin sojin saman Nijeriya ya saki bam ga wasu mutane da ke bikin Mauludi a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda rahotanni suka ce hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 30 ko sama da haka.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp