Tsadar rayuwa ta sa 'yan Nijeriya na jin haushin jami'an gwamnati - Kasshim Shettima


Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce yanzu haka 'yan Nijeriya na jin haushin jami'an gwamnati da sauran 'yan boko ganin irin halin matsin rayuwa da hauhawar farashi ta haddasa a kasar.

Mataimakin shugaban kasar na magana ne a Abuja a wajen taron da cibiyar nazarin tsaro ta shirya.

Jaridar Punch dai ta rawaito cewa wannan ne karon farko da aka ji wani jami'in gwamnati ya amsa cewa ana cikin yanayi na matsin rayuwa a Nijeriya tun bayan da Bola Tinubu ya karbi ragamar tafiyar da kasar a Mayun 2023.

Kasshim Shettima ya ce akwai 'yan Nijeriya masu karamin karfi da ke jin haushin wadanda suke ganin sun samu rufin asiri. Har ya buga misali da cewa a Maiduguri, idan mutum ya sayo sabuwar mota, mutane na mayar da gidansa kamar wani wajen neman gafara ta yadda mutane ke yawan zuwa ziyara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp