An kama mijin da ya yi yunkuri kashe matarsa don ya samu damar sayar da talabijin dinta a Bauchi


Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta sanar da kama wani magidanci mai shekaru 35 da haihuwa da ake zargi da yunkuri hallaka matarsa da tabarya.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce mutumin ya sanar da su cewa ya yi yunkurin aikata hakan ne don ya samu damar sayar da talabijin dinta don ya kara jarin kasuwanci a shagonsa.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Ahmad Wakili.

'Yan sandan dai sun ce mijin ya yi kuruwar cewa barayi sun shiga gidansa, ya ruga ya shiga dakin matarsa ya sanar da ita ta gaggauta rufe fuskarta. Daga nan ya fita, shi ma ya rufe fuskarsa, ya dawo cikin dakin da tabarya, ya fara jibga ma matar tabarya.

'Yan sanda suka ce wanda ake zargin ya amsa laifin cewa ya yi niyyar kashe matar ne don ya samu damar sayar da talabijin da suke kallo a gidan, ya samu kudin da zai kara jarin kasuwanci a shagonsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post