Sanatocin Nijeriya sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen kauyen Tudun Biri


Sanatoci 109 na Nijeriya sun ba da kyautar albashinsu na watan Disamba ga iyalan da bam ya shafa a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna


Sanatocin sun sanar da hakan a ranar Lahadi, lokacin da suka kai ziyarar ta'aziyya da jajanta wa ga iyalai da gwamnatin jihar Kaduna.

Sanata Barau Jibrin da ya jagoranci tawagar ya ce kudin da suka ba da gudunmuwa sun kai Naira milyan 109.

Post a Comment

Previous Post Next Post